KOYI YADDA AKEYIN GRAPHIC DESIGN TA HANYAR AMFANI DA WAYARKA ACIKIN HARSHEN HAUSA A SAUKAKE
Mai yiwuwa ne muntaba ganin wani design da ya burge mu, har ma muna tunanin taya akayi irin wannan abun mai ban shaawa, ko kuma ma mukayi shaawar ace muma mun iya irin wannan design.
Acikin wannan ajin zamu koyi yanda zamuyi designs dinda sukafi wadanda muka taba gani burgewa da ban shaawa
Ni MUHAMMAD BAFFA NASIR (PONT GRAPHICS) nayi shawaran nayi wannan kwas ne saboda ganin yawan mutanen da suke son su koyi Graphic design amma basuda laptop.
Shine nazo da wannan kwas din domin mutane su samo damar koyon Graphic design ta hanyar anfami da wayoyinsu.
Sannan nayi wannan kwas ne acikin harshen hausa saboda yan uwa hausawa su fahimta acikin sauqi
Graphic design shine anfani da fasaha ta zane a isar da tsaqo zuwa ga mutane, ta yarda mutane zasu fahimce saqon ta hanyar gani da idanun su ba sai sun saurari wani abu ba.
Acikin wannan ajin zamu koyi Graphic Design a saukake, daga matakin yan koyo zuwa zama kwararre a harkar graphic design.
Zamu koyi yadda ake yin
Darussan mu an tsara su ne ta yadda kowa zai iya fahimta acikin sauqi.